Amimu ya shaki iskar 'yanci: Yadda aka mika matashin ga iyayensa daga magarkama


Rahotanni sun karade Najeriya na yadda uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha ya amince da janye kara tare da kashe maganar cin zarafin da ta shigar kan wani matashin dan makaranta. Legit.ng ta ruwaito.

Bayan haka ne kuma iyayen dalibin da sauran daginsa suka bayyana dalla-dalla yadda aka ba da umarnin sakinsa tare da kashe maganar ba tare da sake dago ta ba.

Idan baku manta ba, Aminu Muhammadu, dalibi a jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya fito shafin Twitter ya yi kalaman gatsali ga uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari.

Wannan yasa aka kamo shi daga jihar ta Jigawa, aka shilla dashi Abuja domin gurfanar dashi a gaban kotu bisa laifin bata sunan uwar gidan shugaban kasa.

Yadda aka sako Aminu

Wani wakilin BBC Hausa ya bibiyi lamarin don gano halin da ake ciki, da kuma tabbatar da maganar sakin matashin daga iyayensa.

A wani sakon murya da Legit.ng Hausa ta samo daga BBC Hausa da ke bayyana yadda aka sako matashin, an ce tuni aka ba warware batun karar tare da mika matashin ga iyayensa.

A cewar sautin muryar, an dauko Aminu daga magarkamar Suleja inda aka ajiye shi tare da zarcewa dashi ofishin kwamishinan ‘yan sandan yankin babban birnin tarayya Abuja.

An ruwaito cewa, an ga Aminu tare da ‘yan sandan da ke Abuja da shugaban kungiyar daliban Najeriya (NANS) Usman Barambu.

An ga Aminu cikin damuwa da tsoro

A cewar majiyar, an ga Aminu cikin damuwa da gajiya, alamun da ke nuna har yanzu yana cikin wani yanayi na tashin hankali.

A cewar iyayensa, wannan ba zai rasa nasaba da tsare shi da aka yi na tsawon kwanaki ba, kuma haka suna hana dan jarida tattauna da matashin kan halin da ya shiga.

Sun bayyana bukatar a ba dan su damar ya huta tukuna kafin a fara yi masa duk wasu tambayoyin abubuwan da ya gamu dasu daga kama shi zuwa sakinsa.

A cewar rahoto, Yaya Isa, wani aminin mahaifin Aminu ya karbo shi daga hannun ‘yan sanda, kuma daga nan ya zarce dashi gida.

A cewar Yaya Isa:

“Gaskiya an saki Aminu kuma yanzu haka Aminu yana tare da mu yana gida. Mu a matsayinmu na iyayen yaro, za mu yi masa magana kada ya sake irin wannan abu ba ma a uwar gidan shugaban kasa ba, a kan kowa ma, Insha Allahu ba za a sake yinshi ba.

“Ga ‘yan Najeriya da suka taya mu jajen wannan al’amari muna musu godiya kuma Allah ya kare ya tsayar da abin haka.”

A tun farko kun ji cewa, kungiyar dalibai ta Najeriya ta ce za ta rikita kasar nan da zanga-zanga idan aka gaza sako Aminu kafin 5 ga watan Disamba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN