Zaben 2023: Akwai yuwuwar ‘yan siyasa su yi amfani da ‘yan daba wajen yakin neman zabe – DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sanar da ‘yan Najeriya cewa da alama ‘yan siyasa za su yi amfani da ‘yan daba a yakin neman zaben 2023.


Daraktan DSS na Kaduna, Mista Abdul Enachie ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da rahoton yanayin tsaro na kwata na biyu da na uku a jihar.

Daily trust ta ruwaito cewa Enachie ya ce akwai bukatar gwamnati ta dauki lamarin da muhimmanci ta hanyar daukar matakan wayar da kan matasa kan yadda za a rika amfani da su a matsayin ‘yan daba a jihar da sauran sassan kasar nan.

Da yake bayyana bukatar mazauna yankin su rika isar da bayanai ga jami’an tsaro, Daraktan DSS ya kuma bukaci sojoji da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yakar ‘yan ta’adda a yankunan kamar Birnin Gwari da sauran wuraren da suke tashe-tashen hankula.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kammala hanyar Kaduna zuwa Abuja da babbar hanyar Birnin Gwari domin hakan zai taimaka wajen inganta harkar tsaro a hanyoyin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN