Yadda makiyayi ya kashe dan'uwansa bafulatani, ya jefa gawarsa cikin buhu kuma ya sace dabbobinsa


Wani bafulatani da ake kyautata zaton makiyayi ne ya shiga komar yan sandan Najeriya kan zargin kashe dan'uwansa Bafulatani tare da sace dabbobinsa a jihar Enugu. Legit.ng ta wallafa.

SaharaReporters ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne a garin Imama, karamar hukumar Ezeagu ta jihar ranar Laraba.

Ana zarginsa da kashe mutumin tare da jefa gawarsa cikin jaka kuma ya daura kan babu dinsa yana kokarin kaita inda zai jefar yayinda mutan unguwa suka damkeshi.

Daga baya aka mikashi ofishin hukumar yan sanda dake Ezeagu.

Wani mazaunin unguwar a jawabin da yayi yayin daura faifan bidiyon labarin a wani shafin yan asalin jihar Enugu ranar Laraba yace:

"Dubi yadda Fulanin nan ke tada rikici a unguwannin Enugu don Sojoji su kawo mana hari."

"Wannan Fulanin dake cikin motar yan sandan ya kashe dan'uwansa Fulani kuma ya kwashe shanunsa."

"An gansa kuma aka kama shi sannan aka mikashi hannun yan sanda. Wannan abu ya faru a Ezeagu."

An yi yunkurin jin ta bakin Kakakin yan sanda jihar Daniel Ndukwe amma abin ya ci tura.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE