Wata mata ta fille kan jaririnta dan wata 11 a Cross River


Rundunar ‘yan sanda a jihar Cross River ta kama wata mata da har yanzu ba a bayyana sunanta ba bisa zargin fille kan jaririnta dan wata 11 a unguwar Yonen da ke Ugep, karamar hukumar Yakurr a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba.

Da take tabbatar da kamun ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Irene Ugbo, ta ce wasu ’yan daba sun kusa kashe wadda ake zargin bayan sun kama ta.  Ta kara da cewa za a mayar da shari’ar daga Ugep zuwa sashin kisan kai domin gudanar da bincike mai inganci.

An tattaro cewa mahaifiyar ‘ya’ya biyu ta yi amfani da adda wajen yanke kan jaririn.  Wani ganau ya ce dan matar mai shekaru takwas ya tayar da hankali game da kisan, wanda ya ja hankalin makwabta.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN