Wani mutum ya rataye kansa har ya mutu a gadar sama (Hotuna)


Wani mazaunin Bayelsa, Cleopas Donbigstar ya shawarci mutane da su rika duba ‘yan uwansu a koda yaushe.

Ya ba da shawarar ne a lokacin da ya raba hotunan wani mutum da ya kashe kansa ta hanyar rataya a gadar sama da ke kusa da gidan man NNPC da ke titin Sanni Abacha Expressway a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan sandan sun kwashe gawar daga wajen aka ajiye ta a dakin ajiye gawa na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya.


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN