Type Here to Get Search Results !

Na kashe N1m, ina kwana da karuwai biyu a kullum, tsawon wata daya – wanda ake zargi da garkuwa da mutane

Na kashe N1m, ina kwana da karuwai biyu a kullum, tsawon wata daya – wanda ake zargi da garkuwa da mutane


Jami’an FIB-IRT na Yan sanda sun kama wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane ne da suka yi garkuwa da matar wani fitaccen dan kasuwa a Rivers, watanni takwas da suka gabata.

Matar mai suna Misis Hussana Adamu, tana kan hanyarta ne ta ajiye ‘ya’yanta a makaranta lokacin da masu garkuwa da mutane dauke da makamai suka tare ta a kusa da filin wasa na Casablanca, yankin karamar hukumar mulki ta Fatakwal, jihar Ribas.

An biya N20m zaman kudin fansa. Sai madugun kitsa harin mai suna Isiaka daga jihar Adamawa mai sana'ar sayar da Tantabara da Talotalo ya ce:

"Na kwana a wani otal, na dinga gayyatar karuwai kowane dare na wata daya.

Na kwana da ashawo akalla biyu a kowane dare tsawon wata daya kuma na biya su Naira 20,000 kowanne.

"Na yi amfani da ragowar Naira 300,000 wajen shuka masara a kauyen", in ji shi, yana mai cewa wannan ne karon farko da ya fara yin garkuwa da mutane.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies