Tsohuwar abokiyar gidan Big Brother Naija, Uriel Oputa, ta ce yanzu tana sha'awar maza da suka kwana biyu saboda samari 'yan shekara 30 suna 'dandana wa mata barkono'. Shafin isyaku.com ya samo.
"Abin dariya ne ban taba sha'awar mazan da ba su yi aure ba. Amma yanzu samari masu shekaru 30 na dandana mana barkono daga bisani," ta rubuta a labarinta na Instagram a ranar Litinin, 14 ga Nuwamba.
Jarumar wadda tun farko ta yi tsokaci kan matsalolin dangantaka, ta kara da cewa; "Bari naje na tambayi aunties ko 'yan ajin su basu da aure. Everyday pepper pepper Ah Ah. My guys cool o down."