Madigo tsakanin mata da yadda lamarin ya kasance a zamantakewa

Madigo tsakanin mata da yadda lamarin ya kasance a zamantakewa

Daga Abdul Tonga


Kalmar Madigo kalmace da take nufin saduwar mace da mace domin biyan bukatarsu na sha'awar jima'i. 

Duk da yake bazan iya kawo yadda Kalmar ta samu asali a harshen Hausa ba, sai dai kalmar ta yi fice kamar yadda aka lakabawa mata masu irin wannan dabi'a.

Ita dai wannan bakar dabi'a ta madigo dabi'ace ta yadu a dukkan duniya, babu yanki, nahiya ko kabilar ba a samun mata masu neman junansu, wasu kasashen ma ba ma saduwar suka aminta dashi ba, sun ma baiwa masu irin wannan hakin damar auren junansu domin zama irin na miji da mata.

Haka kuma an samu wasu dariku irin na addinin Nasara da wasu bangaren sun aminta da auren jinsi a addinance kamar yadda wasu dariku a boye suke baiwa masu sha'awa ko aikata irin wannan mugun halin fatawa a boye na halasta lamarin na madigo.

A shekarun baya can da suka gabata wannan dabi'ar ba a sanshi ba a tsakanin wannan al'umar, da tafiya tayi tafiya sai aka soma tsintarta a cikin 'ya'ya mata musamman wadanda suke makarantu kwana, saboda wata al'ada dake tsakanin dalibai mata na 'daughter and mummy' hakan ya zarce zuwa 'Darling', daga nan fa abu yayi ta girmama yayi ta fadada. Tun suna boyewa saboda ana hantararsu har ya dawo dai babu kunya babu tsoron Allah suke al'amuransu babu kunya kuma babu tsoro.

Abunda zai iya baiwa masu karatu mamaki shi ne, a baya 'yan mata marasa aure suke yin madigo, yanzu abun ya karfafa ya bunkasa ya girmama matam aure, zaurawa har ma da tsoffi suna cikin na gaba gaba a madigo.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN