Kuma dai: Yan daba sun kai farmaki wurin gangamin yakin neman zaben Atiku a Gombe, sun yi barna


Aƙalla mutane uku ne suka samu raunuka ranar Litinin a wata arangama tsakanin 'yan Daban gari, Kalare Boys da magoya bayan Atiku, waɗanda suka je Gombe yakin neman zaɓe. Legit.ng ta ruwaito.

Punch ta tattaro cewa an yi kaca-kaca da ababen hawa huku da suka haÉ—a da Motar Bas, Karamar Mota da Keke Napep lokacin da Yan Daban suka mamayi mutane a Titin Filin Pantami.

Sakataren watsa labarai na PDP a jihar, Usman Muritala, yace ba shi da masaniya saboda ba'a sanya shi cikin masu tsara gangamin yakin neman zaɓen ba.

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bana wurin kuma na halarci filin taron ne a matsayin É—an jam'iyya don haka na nemi wuri na zauna kamar kowa domin na kalli abinda ke wakana. Akwai matsala babba ta rabuwar kai a jam'iyya."

Meya haddasa rikicin?

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa danbarwar ta fara ne loacin da Atiku tare da 'yan tawagarsa suka fice ta Kofar mai lamba ta biyu a Filin wasan Pantami suka nufi jihar Bauchi.

'Daga nan ne Yan Kalare É—auke da Adduna, Wukake da wasu makamai suka farwa magoya bayan PDP waÉ—anda ke kokarin fita daga wurin su koma gidajensu.

An ce jami'an yan sanda dake tsaron Kofa mai lamba É—aya cikin hanzari suka kai É—auki Kofa mai lamba biyu domin baiwa magoya bayan tsaro bayan sun koma cikin fili.

Da yawan mutanen sun tsaya cirko-cirko a cikin filin suna jiran 'yan sanda su shawo kan komai sabida 'yan kalare sun toshe hanyar zuwa Kasuwar Pantami da Gidan gwamnati suna farmakan masu wucewa.

Bisa tilas wasu matan PDP suka haÉ—a da Motar 'yan sanda ta musu rakiya domin guje wa matsala daga Yan daban Kalare.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Gombe, ASP Mahid Abubakar, yace yana cikin wata ganawa don haka ba zai iya tabbatar da abinda ya faru ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN