Hukumar NIS ta kwato sama da katin shaida na kasa 500 da PVC daga hannun wasu ‘yan kasashen waje a Katsina


Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta ce an karbo katin shaidar dan kasa guda 513 da katin zabe na dindindin (PVCs) daga hannun ‘yan kasashen waje a Katsina. Shafin isyaku.com ya samo.

Kelechi Ekeoba-Jones, kontrolan NIS a jihar, wanda ya bayyana hakan ga NAN a ranar Litinin, 14 ga watan Nuwamba, 2022, yayin wata ganawa da manema labarai a sabuwar rundunar da aka kafa a kan iyakar Jibia.

Ya ce rundunar ta musamman ta kan iyaka da ke Jibia ta kwato PVC guda 202 da katin shaida na kasa 311 daga hannun wadanda ba ‘yan Najeriya ba a jihar.

“An samu wasu ‘yan kasashen waje dauke da katin zabe na tarayyar Najeriya da katin shaidar dan kasa da aka ba su a jihohi daban-daban na kasar,” in ji shi.

“Katin zabe da katin shaida na kasa guda 513 ne aka karbo daga hannunsu a sassa daban-daban na rundunar.

“Saboda haka, muna neman goyon bayan hukumar zabe ta kasa (INEC) da ta ba mu hadin kai a duk lokacin da za a sake gudanar da rajistar masu zabe.

Jami’an shige da fice ne kawai za su iya tantance baki ta hanyar dabarun mu a duk lokacin da suka zo yin rajista a kowace cibiyar rajista a fadin kasar nan.

“Muna kira ga INEC, a duk lokacin da za a yi rajista, su nemi taimakon jama’armu, don kaucewa yi wa ‘yan kasashen waje rajista.

“Don haka kuma, hukumar da ke da alhakin yin rajistar katin shaidar dan kasa, ya kamata ta rika daukar karin jami’an mu a duk lokacin da za a fara atisayen saboda yana da matukar muhimmanci,” ya kara da cewa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN