Hafsan dan sanda ya yi wa wata mata Safeton yar sanda tsirara ya lakada mata duka a jihar kudu, IGP ya ce a gudanar da bincike kan zargin

Hafsan dan sanda ya yi wa wata mata Safeton yar sanda tsirara ya lakada mata duka a jihar kudu, IGP ya ce a gudanar da bincike kan zargin


Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun, CP Olaleye Faleye, da ya binciki zargin cin zarafin wata mata Insifekta Olorunsogo Bamidele da DCO ya yi a Ode Omu Jihar Osun.

A cikin wani faifan bidiyo da ake ta yadawa, jami’ar ‘yan sandan ta zargi maharin da ta bayyana sunansa da Ajayi Mathew da tube ta tsirara tare da lakada mata duka saboda ta ki amincewa da shi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta karanto wani bangare.

 'Za mu jira rahoton binciken daga rundunar 'yan sandan jihar Osun kafin a dauki matakan da suka dace.  Duk da haka muna tabbatar wa jama'a cewa za a yi adalci a cikin shari'ar, don kare ainihin dabi'u da martabar aikin NPF.  ''

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN