Gwamnan Arewa ya ketare rijiya da baya, yan sanda 2 sun jikkata bayan hatsarin mota ya rutsa da tawagarsa


Yan sanda biyu sun jikkata bayan da wata babbar mota ta afka wa ayarin motocin Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa
.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan Fintiri da wasu daga cikin ‘yan Majalisarsa sun bar wani daurin aure a Masallacin Agga da ke unguwar Dougirei a Yola, babban birnin jihar.

An dai yi zargin cewa babbar motar ta rasa yadda za ta yi, ta kuma kutsa cikin ayarin motocin guda biyu cikin sauri.

Gwamnan wanda da kyar ya tsallake rijiya da baya, ya fito daga motarsa ​​ya gargadi direban babbar motar kafin ya bar wurin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN