Type Here to Get Search Results !

Dan Keke Napep ya sha duka a hannun abokin sana'arsa har ya mutu


Ana zargi an yi wa wani dan adaidaita watau Keke Napep dukan tsiya har lahira a hannun abokin aikinsa a lokacin da aka samu rashin fahimtar juna tsakanin ma’aikatan a yankin Oke-Aro da ke karamar hukumar Akure ta Kudu a jihar Ondo a karshen mako.

A cewar rahotanni, mai Keke Napep da ba a tantance ba da abokin aikinsa sun yi zazzafar gardama wadda ta rikide zuwa fada da ya kai daya daga cikinsu ya fadi.  An garzaya da shi wani asibitin da ke kusa inda aka farfado da shi amma daga baya ya rasu a ranar Lahadi 13 ga watan Nuwamba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Funmi Odunlami, ya ce an umurci jami’an hukumar da su binciki lamarin.

“Mutanen da ke kusa da wurin fadan ne suka garzaya da mutumin, zuwa wani asibitin da ke kusa da shi inda aka kwantar da shi.  Wanda aka kashe ya fadi ne sakamakon fadan da aka yi ranar Asabar kuma an tabbatar da mutuwarsa da sanyin safiyar Lahadi a asibiti.” Inji shi

Ya ce an kai rahoton lamarin ne a hedikwatar mu mai suna ‘B’ Division da ke Akure kuma an fara bincike kan lamarin.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies