Dalibar da ake kyautata zaton ita ce dalibar firamaren da ta fi tsufa a duniya, Priscila Sitienei, ta rasu. BBC ta ruwaito.
Marigayiyar wadda aka fi sani da sunan Gogo (wato kaka a harshen Kalenjin) ta rasu ne tana da shekara 99 a ranar Laraba a kasar Kenya.
Dattijuwar daliba ce a makarantar Vision Preparatory School da ke garin Ndalat kuma ta shirya rubuta jarabawar kammala firamare shekara mai zuwa, inda za ta cika shekara 100.
Jikanta mai suna, Sammy Chepsiror, ya shaida wa BBC cewa Gogo ta fara rashin lafiya ne ranar Laraba bayan ta dawo daga makaranta – inda ta ce masa kirjinta na ciwo.
Shekaru da dama da suka wuce, marigayiyar tana aiki ne a matsayin ungozoma a kauyensu.
Rubuta ra ayin ka