Dalibai sun yi wa shugaban makarantar sakandare dukan tsiya bayan an kama shi turmi tabarya da wata daliba


Wani mataimakin shugabar makarantar Sakandare ta Afirka ta Kudu ya samu hukunci nan take daga hannun katta bayan an kama shi da wata daliba turmi tabarya
.

An yi wa mataimakin shugaban makarantar sakandaren Kgagatlou a Polokwane, Limpopo duka bayan an kama shi yana lalata da wata daliba a lokacin makaranta.

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafin Twitter, an ga jama'a na dukan mataimakin shugaban makarantar yayin da yake daute a wani karfe.

An kuma yi zargin cewa wannan ba shi ne karon farko da aka kama shi yana aikata ta'addanci a makarantu ba.  Rahotanni sun ce an dauke shi daga wata makaranta kafin ya zama mataimakin shugaban makarantar sakandaren Kgagatlou.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN