Da ɗumi-ɗumi: An rufe hanyar Kano zuwa Ɓaɓura sakamakon rikicin manoma da makiyaya


An rufe hanyar Kano zuwa Ɓaɓura daidai garin Kunya sakamakon rikicin manoma da makiyaya da ya ɓarke a yammacin yau Talata.

Bayanan da Freedom Radio ta samu sun nuna cewa kusan mako guda kenan ana ɗauki ba daɗi a tsakani.

Sai dai a yammacin yau Makiyaya sun kai mummunan hari a unguwar Kuka Bakwai da ke Kunya, inda suka hallaka mutum guda tare da jikkata da dama.

Yanzu haka an rufe hanyar.

Dagacin Kunya Musa Zangi II da Freedom Radio ta samu a asibiti ana shirin ɗaukar gawar wanda ya rasu, ya ce an hana shi magana a kai.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE