Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama wasu mutane biyu da laifin yi wa wasu kananan yara biyu fyade a kananan hukumomin Danko/Wasagu da Augie (LGAs) na jihar. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Daya daga cikin wadanda ake zargin Mista Christopher Pills mai shekaru 30 a garin Bena da ke karamar hukumar Danko/Wasagu ta jihar an kama shi ne bayan mahaifin yarsa mai shekaru 9 da haihuwa, Mista Lawrence Johnson, ya ruwaito cewa Pills ya lalata ‘yarsa.
Shi kuma wanda ake zargin Anas Dantalli mai shekaru 19 a Nawada Illela Kwaido a karamar hukumar Augie, an kama shi ne bayan wani mai suna Mista Rugga Aliyu na Mashekari Illela Kwaido, karamar hukumar Augie, ya kai rahoto a hedikwatar ‘yan sanda da ke Augie cewa wanda ake zargin ya bi ‘ya’yansa ne a lokacin da suke kiwon awaki da tumaki a cikin daji, ya yi wa daya daga cikinsu fyade.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmed Magaji-Kontagora ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI