Da dumi-dumi: Maigida ya yi wa surukinsa dan karen duka ya caka masa kwalba a kai, duba dalili

Kotu ta tsare wani mutum bisa zarginsa da daba wa surukinsa wuka


Wata Kotun Majistare ta Abeokuta a ranar Alhamis ta tsare wani mutum mai shekaru 43, Tunde Odedo bisa zarginsa da daba wa surukinsa kwalba a kai, har sai an kamala bincike.

 Odedo, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, ana tuhumarsa da laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma kai hari.

 Alkalin kotun, O.A Akamo-Oyede, wanda bai amsa rokon Odedo ba, ya amince da bayar da belinsa a kan kudi N50,000 tare da mutum daya mai tsaya masa.

 Akamo-Oyede ya dage sauraron karar har zuwa ranar 23 ga watan Nuwamba.

 Tun da farko, Dan sanda mai gabatar da kara, Insp Evelyn Motim, ya shaida wa kotun cewa Odedo ya aikata laifin ne a ranar 30 ga watan Oktoba da misalin karfe 7:50 na yamma a AbuIe Ijaye daura da titin Ayetoro a Abeokuta.

 Motim ya ce Odedo ya daba wa Mista Adebayo Adeoye, mahaifin mamatarsa fasashen kwalba a kansa.

 Ta ce an gayyaci Odedo ne domin ya shiga tsakani a wata matsala ta aure, kuma ya hada baki da wasu, inda suka yi ta dukan surukansa.

 Ta kara da cewa wasu surukai kuma sun samu raunuka.

 Ta ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 516 da 355 na dokokin laifuka na Ogun 2006.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN