Buhari ya fusata da tashe-tashen hankula masu nasaba da yaƙin neman zabe a fadin kasar nan ya gargadi yan siyasa

Buhari ya fusata da tashe-tashen hankula masu nasaba da yaƙin neman zabe a fadin kasar nan ya gargadi yan siyasa


Yayin da ya fusata da tashe-tashen hankula masu nasaba da zabe a fadin kasar nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan siyasa kan illar ayyukansu, inda ya gargade su da su danne ‘yan baranda ko kuma su fuskanci koma baya daga jami’an tsaro. Jaridar vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta damu da yadda ‘yan siyasa ke shiga tashin hankali, inda ya ce a cikin wata guda an samu aukuwar irin wadannan abubuwa guda 32.

Shawarar ta shugaban ta zo ne a daidai lokacin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kuma yi Allah-wadai da yawaitar tashe-tashen hankula a kasar nan, musamman dangane da yakin neman zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa, inda ta ce ta bi diddigin tashe-tashen hankula 50 na yakin neman zabe a jihohi 21.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE