Boka ya bindige kwastoma har Lahira yayin da yake gwajin layar kare harsashi a jikinsa


Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta kama wani boka dan shekara 23 mai suna Odoh Emmanuel, wanda ya bindige wanda yake kwastoma a lokacin da yake gwada ingancin maganin bindiga da ya tanadar wa marigayin. Shafin isyaku.com ya samo.

Kakakin rundunar Yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba, 2022, ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Isi-Uzo da ke jihar.

A cewar PPRO, wanda ake zargin ya harbi marigayin, Onunze Benedict, da wata bindigar da aka kera ta gida a cikin wurin ibadar sa a lokacin da yake gwada karfin maganin bindigar.

“A ranar 16/11/2022 da misalin karfe 11:00 na rana, jami’an ‘yan sanda da ke aiki a sashin ‘yan sanda na Isi-Uzo na rundunar ‘yan sanda sun kama Odoh Emmanuel (Namiji kuma boka dan asalin jihar) mai shekaru 23 a kauyen Umuaram da ke unguwar Ikem a karamar hukumar Isi-Uzo.  Sanarwar ta kara da cewa, saboda harbi da kuma kashe wani baligi mai suna Onuze Benedict, dan kabilar Eha-Amufu a karamar hukumar. 

“Bincike na farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya amsa laifin yin amfani da bindiga da aka kera a cikin gida wajen harbi da kuma kashe kwastoma a wurin ibadarsa a wurin da aka ambata, a lokacin da yake gwada bajintar kariya daga harbin bindiga da ya shirya masa.

"An gano bindigar, yayin da ake ci gaba da bincike a sashin kisan kai na CID na jihar Enugu."

 Za a gurfanar da wanda ake zargin da zarar an kammala bincike.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN