Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Ahmed Tinubu, ya bayar da dalilan da ya sa ya daina maida hankali kan kasidu da labarai da kuma batutuwan da suka taso a shafukan sada zumunta. Jaridar Vanguard ta ruwaito.
Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana cewa karanta labarai a shafukan sada zumunta na ba shi ‘hawan jini’.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo da daya daga cikin abokansa, Ademola Oshodi ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A cikin faifan bidiyon, tsohon gwamnan jihar Legas ya ce yakan yi fushi a duk lokacin da ya karanta labarai a shafukan sada zumunta.
“Ba na kara karanta labaran kafafen sada zumunta; suna yi min zagin fitar hankali. Idan na karanta, yakan haddasa min tashin hankali kuma da fushi".
“Ba na karanta shi, don haka idan ina son jin wani abu; 'Ya'yana ko ma'aikata na za su faÉ—i wannan nayan sun karanto, in na gaji, na ce don Allah a manta da shi."