Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanar da shirinta na gudanar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 a jihar Gombe a ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba. Legit.ng ta wallafa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato, Vanguard ta rahoto.
An shirya gudanar da gangamin kamfen din ne a babban filin wasa na garin Gombe da misalin karfe 11:00 na safiyar gobe Litinin.
Tambuwal ya roki mambobin PDP da su halarci gangamin Atiku na Gombe
Tambuwal ya bukaci daukacin zababbun mambobi da masu biyayya ga jam’iyyar da su hallara domin hada hannu da Atiku Abubakar da Ifeayi Okowa wajen farfado da Najeriya, rahoton TheCable.
Sanarwar ta ce:
"Ku hada hannu da Atiku Abubakar don kwato Najeriya.
“Wannan don gayyatan daukacin zababbun gwamnonin PDP, mambobin kwamitin aiki na PDP ta kasa, yan majalisar dokokin tarayya, mambobin kwamitin NEC na PDP, mambobin kwamitin amintattu na PDP, shugabannin PDP rassan jiha, tsoffin gwamnoni, tsoffin ministoci, yan takarar PDP, masu ruwa da tsari zuwa jihar Gombe don gangamin yakin neman zaben shugaban kasa.”
A kwanan nan ne PDP ta yi gangamin kamfen dinta a Borno wanda ya samu halartan dandazon mutane inda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar ya ba mutanen jihar tabbacin samun kulawar gwamnati idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.
Sai dai kuma, wasu bata gari sun farmaki tawagar Atiku a wajen gangamin na jihar Borno.
Mai ba Atiku shawara , Paul Ibe, ya yi ikirarin cewa magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne suka kai farmakin.
Gwamnonin G-5 da jiga-jigan PDP sun shiga labule
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnonin PDP wanda ake yiwa lakabi da G-5 suka shiga labule tare da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar.
Akwai rashin jituwa sosai tsakanin gwamnonin babbar jam'iyyar adawar da dan takararta na shugaban kasa tun bayan kammala zaben fidda gwani.
Sun ce lallai sai shugaban jam'iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, ya sauka daga kan kujerarsa kafin su yiwa Atiku kamfen.