2023: Manyan kungiyoyin magoya bayan Atiku 10 sun canza shawara, sun koma bayan APC da Tinubu


Ƙungiyoyin magoya baya 10 da suka yi mubaya'a ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, sun canza shawara, sun koma jam'iyyar APC. Legit.ng ta ruwaito.

Ƙungiyoyin da suka ɗauki matakin sun haɗa da, Atiku Support Organisation, PDP Transformation Ambassadors, Atiku Abubakar Kawai, PDP Mobilisers Initiative, Kasa Daya Al’umma Daya, da Atiku-Okowa Frontiers Movement.

Sauran su ne, G7 Business Community, Katsina Biyayya Forum, Atiku Women and Youth Initiative da kuma Atiku Nigeria Transformation Ambassadors, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da mataimakin shugaban APC na ƙasa na shiyyar arewa ta yamma, Salihu Lukman ne suka karɓi masu sauya shekar hannu biyu.

Yan siyasan sun rungumi APC ne a hukumance bayan wani taron gaggawa da ya kwashe awanni, a cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin APC na shiyyar arewa ta yamma, Musa Mailafiya Mada.

Sanarwar wacce ta samu haɗin guiwar sa hannun kakakin kwamitin kamfen Tinubu na shiyyar, Muhammed Shehu, ta ce:

"Waɗannan ƙungiyoyin sun sadaukar da kansu don goyon bayan Atiku da PDP amma aka yi watsi da su, sun zuba dukiyarsu da lokacinsu kan burin Atiku tun 2015 amma babu wani sakamako."

"Alaƙa mai tsamin da ta shiga tsakaninsu ya tilasta musu hijira daga PDP da ɗan takararta na shugaban kasa, kana suka ayyana mubayi'arsu ga APC da Bola Ahmed Tinubu."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN