Type Here to Get Search Results !

Yan sanda sun ceto wani mutum tsirara da aka kulle a wani daki tsawon shekaru 20 a Kaduna

Yan sanda sun ceto wani mutum tsirara da aka kulle a wani daki tsawon shekaru 20 a Kaduna


A ranar Laraba ne ‘yan sanda suka ceto wani dattijo mai shekaru 67 da aka kulle a daki sama da shekaru 20 a Kaduna.

An gano mutumin ne tsirara kuma an kulle shi a wani daki a wani gida da ke hanyar Bayajidda a cikin garin Kaduna.

Mazauna ginin sun gudu a lokacin da tawagar ‘yan sanda suka isa gidan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Jalige ya ce wasu jami’an kiwon lafiya na muhalli ne suka fara gano mutumin mai suna Ibrahim Ado da ke gidan a kulle.

“Sun kai rahoto ga sashin ‘yan sanda na Magajin Gari da kuma Kwamishinan‘yan sandan ya umarci jami’an da su yanta wanda abin ya shafa.

 "Ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin don bayyana al'amuran da suka shafi lamarin da kuma dalilin da ya sa aka kebe mutumin na tsawon wannan lokaci," in ji shi.

Jalige ya ce an kai wanda aka kulle asibiti domin a duba lafiyarsa.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies