Wani mutum ya kashe kansa bayan barayi sun sace masa baburan adaidaita sahu guda biyu

Wani mutum ya kashe kansa bayan barayi sun sace masa baburan adaidaita sahu guda biyu


Wani matashi mai suna Bulus Asuma mai shekaru 25 ya kashe kansa a garin Jos na jihar Filato, bayan baragi sun sace adaidaita sahu da ya saya guda biyu.

Asuma na Angwan Rukuba da ke karamar hukumar Jos ta Arewa ya rataye kansa a dakinsa a lokacin da ya dawo gida a ranar da wani dauke da makami ya kwace masa babur na biyu bayan na farko. 

Majiyoyin iyalan sun ce marigayin ya karbi babur adaidaita sahu a hannun wata mata a farkon shekarar a kan sayen haya. An sace masa keken napep, kuma matar da ya sayi keken a hannunta ta kulle shi har tsawon mako guda a wajen jami'an tsaro . Marigayin ya biya wasu makwanni kuma ya kasa ci gaba saboda ya kare. A wannan karon ya tuntubi wani mutum ya ba shi wani babur Keke napep don yin aiki kuma yana aika kuɗi a kowace rana don samun damar samun kuɗi don biyan tsohon ma’aikacin sa. Abin bakin ciki a ranar 13 ga Oktoba, yayin da yake dawowa daga aiki, wani mutum dauke da makami ya kai masa hari, wanda ya kwace masa babur din.

‘Yan uwansa sun ce ya koma gida ne kuma ya yi barazanar kashe kansa amma ba su dauke shi da muhimmanci ba. Sai dai daga bisani ya rataye kansa da igiya a cikin dakinsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan sanda na gudanar da bincike kan lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN