Tashin hankali yayin da wani hadari ya lakume rayukan mutane sama da 10 a jihar Arewa

Tashin hankali yayin da wani hadari ya lakume rayukan mutane sama da 10 a jihar Arewa


Wani Ibtila'i ya auku a kauyen Hawan Jaki da ke Titin Alkaleri-Gombe a ƙaramar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi ranar Asabar yayin da mutane 11 suka mutu a haɗarin mota. Legit.ng ta ruwaito.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra (FRSC) na yankin Bauchi, Mista Yusuf Abdullahi, ya shaida wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) cewa wasu mutum 8 sun jikkata sakamakon haɗarin.

Yace hatsarin ya rutsa da wata Motar haya ta kamfanin Yankari Express da kuma wata Motar Ɗangote, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Menene ya haddasa haɗarin?

Mista Abdullahi ya jingina musabbabin abinda ya jawo hatsarin da mummunna tuƙi mai haɗari, inda yace:

Maza matasa 20 ne mummunan haɗarin ya rutsa da su, mutum Tara daga ciki suka mutu nan take a wurin yayin da Likitoci suka tabbatar da cikawar wasu biyu a babban Asibitin Alkaleri."

"Haka nan wasu mutum Takwas sun ji raunuka iri daban-daban kuma yanzu haka suna kwance a Asibitin Alkaleri ana kulawa da lafiyarsu. Jami'ai sun kai gawarwakin wadanda suka Mutu asibitin."

Kwamadan FRSC, Mista Abdullahi, ya kara da gargaɗin matafiya cewa a ko da yaushe su rika kokarin kiyayen ƙa'idoji da dokokin tuki yayin da suka hau kan titi, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

Gwamna Bala Muhammed na Bauchi ya umarci Ciyamomi 20 su sauka daga kujerunsu bayan wa'adinsu ya ƙare.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar, umarnin ya shafi mataimakan ciyamomi, Sakatarori da Kansiloli.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN