Mun nemi afuwar 'yan Najeriya saboda ba tabbas ko mun biya buƙatunsu - Aisha Buhari
Matar Shugaban Najeriya Aisha Buhari, ta ce saboda yawan burin da 'yan Najeriya suka ci a kan gwamnatinsu, ba ta da tabbas ko sun biya wa 'yan ƙasar buƙatun nasu.
Rahotanni sun ambato ta tana bai wa 'yan Najeriya haƙuri game da wahalhalun rayuwa da suke fuskanta yayin addu'o'i na musamman da ta shirya a ranar 1 ga watan Oktoba don bikin cika shekara 62 da samun 'yancin-kan ƙasa.
A farkon watan Oktoban ne jam'iyyarsu ta APC mai mulkin ƙasar ta naɗa Aisha Buhari a matsayin jagorar tawagar kamfe ta mata a matakin takarar shugaban ƙasa.
Ga fassarar amsoshin tambaya takwas da aka yi mata yayin hirar da aka naɗa a fadar shugaban ƙasa da ke Birnin Tarayya Abuja.
Me ya sa kika nemi afuwar 'yan Najeriya?
"Burikan da aka ɗora mana suna da matuƙar yawa. Mutane sun ɗora burika a kanmu, kuma wataƙila bayan shekara bakwai ba mu cika musu dukkan burikan ba.
"Allah ne kaɗai ya san abin da ke zuciyar mutane. A matsayinka na ɗan Adam, ba za ka iya cewa ka yi daidai ba, ko kuma ka ce ka yi abin da ya kamata. Saboda haka gwamnatin ta yi ƙoƙari, amma ba lallai haka kowa ke gani ba.
"A wajensu sun yi ƙoƙari, Allah kaɗai ya sani. Saboda haka dole mu bai wa 'yan Najeriya haƙuri ko da mun cika musu burinsu ko ba mu cika ba.
A ganinki, a wane ɓangare ne suka fi gazawa?
"Ban sani ba, saboda ni ina gudanar da ofishina tamkar ƙungiyar agaji ne; kawai ina karɓar mutane ne amma ba na harkar siyasa. Abinda nake yi kawai shi ne mara musu baya ta ɓangaren lafiya ko kuma ilimi.
"Ba na bin diddigin abubuwan da suke yi."
Kina ganin akwai yiwuwar APC ta kasa cin zaɓe a 2023?
"Me ya sa za ki yi min wannan tambayar? Tsaf kuwa za mu ci gaba. APC ce za ta ci zaɓe. Da izinin Allah.
Da me kika fi so a dinga tunawa da ke?
"Yi wa al'umma hidima. Muna bai wa yara kayan makaranta. Mun aro wasu abubuwa daga ƙudirorin jam'iyya kuma muka yi amfani da su wajen yaƙin neman zaɓe; bai wa yara abinci ta yadda hakan zai ba su ƙarfin gwiwar zuwa makaranta.
"Mun fuskanci babban ƙalubale saboda lokacin da mijina ya hau mulki ba kuɗaɗe, amma na dage a kan cewa mu ne muka ce za mu yi kuma dole ne mu yi.
Kina ganin za a ci gaba da yin hakan bayan mijinki ya sauka daga mulki?
Tabbas za a ci gaba da yin hakan muddin dai APC ce ke ci gaba da mulki.
Kina da burin tsayawa takara nan gaba?
Na gode wa Allah da ya ba ni damar zama matar shugaban ƙasa. Babban matsayi ne. Na gode wa Allah kuma ina roƙonsa ya sa mu gama lafiya, mu sake miƙa wa gwamnatin APC mulki.
"Ba ni da wani buri na siyasa. Zan zama matar tsohon shugaban ƙasa, me kuma nake nema
Idan kika huta kaɗan fa, sai ki dawo
"Na fi so na ci gaba da hutawa.
Wace shawara za ki bai wa matar shugaban ƙasa mai zuwa? Me za ki faɗa musu wanda ba lallai wani ya faɗa musu ba
"Kar ta yi kwana-kwana, kuma kar ta bari wani ya zo ya mamaye gwamnatinsu. Su saurari mutanen da suka zaɓe su. Dole ne su saurari jama'a
"Kar ta yi wata kwana-kwana a duk halin da ta tsinci kan ta. Kar ta bari wani ya tsara mata rayuwa, ita ce ya dace ta tsara rayuwarta."