Matashi ya shake mahaifiyarsa har lahira saboda ta kira shi dan iska


Wani yaro dan shekara 18 mai suna Tope Momoh wanda ya shake mahaifiyarsa har lahira saboda ta kira shi dan iska, ya gurfana a gaban wata Kotun Majistare da ke Akure bisa tuhumarsa da laifin kisan kai. 

An bayyana cewa Momoh ya amince da kashe mahaifiyarsa mai shekaru 52, Stella, makonni biyu bayan binne ta.

Ya aikata laifin ne a tsakar daren ranar 6 ga Satumba, 2022 a garin Ikakumi Akoko da ke jihar Ondo.

Da yake ba da shaida a gaban Kotu, dan sanda mai shigar da kara, Nelson Akintimehin, ya shaida wa Kotun cewa ba a san musabbabin mutuwar matar ba har sai da danta ya amsa cewa shi ne ya kashe ta.

Akintimehin ya ce; 

"Momoh a cikin ikirari da ya yi, ya ce an tilasta masa ya shaida wa 'yan uwansa cewa ya shake mahaifiyarsa har lahira a lokacin da ta tashe shi da tsakar dare, ta yi masa ruwan tsinuwa tare da kiransa da dan iska."

Laifin a cewar mai gabatar da kara, ya ci karo da sashe na 319(1) na kundin laifuffuka, Cap 37, Vol. II Dokar Jihar Ondo, 2006.

Momoh wanda ya roki gafara lokacin da aka ba shi damar yin magana, ya ce; 

“Ban huta ba tunda aka binne mahaifiyata. Don haka, an tilasta ni in furta cewa na shake ta har ta mutu. Don haka ina so Kotu ta tausaya mani.”

Ba a amsa rokonsa ba sai Alkalin Kotun Mai shari’a Musa Al-Yunnus, wanda ya bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali na Olokuta.

Al-Yunnus ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga Oktoba, 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN