Type Here to Get Search Results !

Mahaifiyar yara 3 ta sheke masoyinta bayan ya kama ta a gidan wani mutum cikin unguwarsu - ISYAKU.COM

Mahaifiyar yara 3 ta sheke masoyinta bayan ya kama ta a gidan wani mutum cikin unguwarsu


Rundunar ‘yan sanda a jihar Edo ta tabbatar da kama wata mata ‘yar shekara 26 da ta kashe masoyinta da wuka har lahira a garin Benin.

‘Yan sanda sun bayyana matar da sunan Gift Obieriei, mahaifiyar ‘ya’ya uku, ‘yar karamar hukumar Ethiope ta Gabas ta jihar Delta.

An tattaro cewa marigayin, Mista Eghosa Iguodala, direban motar bas ne, yana da aure kuma yana da ‘ya’ya hudu.

Marigayi Iguodala da wanda ake zargin sun yi jima'i ne kafin lamarin ya faru a titin Imafidon, Off Upper Siluko Road, Egor Quarters, Benin City da misalin karfe 12 na rana a ranar Litinin, 24 ga Oktoba, 2022.

An ce sun fara soyayya kusan wata guda da ya wuce.

An bayyana cewa matar ta daba wa masoyin nata fasasshiyar kwalba a wuya da bayansa a lokacin da mutumin ya bi ta da adda da ya gan ta a gidan wani da ke unguwar su.

‘Yan sanda sun ce nan take ya zubar da jini har ya mutu, sannan jami’an tsaro sun kwashe gawar tasa jibge da jini zuwa dakin ajiyar gawa.

A cikin wani faifan bidiyo, wata mata da aka daure hannunta a kujerar baya ta mota yayin da ta bayyana kanta a matsayin Gift, daga jihar Delta, mazaunin Uhogua Community a cikin birnin Benin, ta ce marigayin ya gan ta ne a gidan wani sakamakon haka rikici ya barke. 

“Da ya gan ni tare da wani, sai ya zo ya yi mini fada a gidan mutumin.  Ba ni zaune a gidansa, na je ganin wani,” in ji ta.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies