Karo na biyu, TY Danjuma ya yi kira ga yan Najeriya su dau bindigu su kare kansu


Tsohon Ministan Tsaro, Janar Theophilus Danjuma (mai ritaya) a ranar Asabar ya jaddada kira ga yan Najeriya su tashi tsaye su kare kansu daga hare-haren yan bindiga da suka addabi kasar.

TY ya bayyana hakan ne a taron mikawa sabon Aku Uka na garin Wukari, Manu Ali, sandar mulki a garin Wukari, jihar Taraba, rahoton NAN.

Gwamna Darius Ishaku na Taraba ya nada sabon sarkin ne tun 2021 sakamakon mutuwar Sarki Shekarau Angyu da ya kwashe shekaru 45 kan karagar mulkin.

TY Danjuma ya ce kiran da yayi da yan Najeriya shekarun baya na cewa su kare kawunansu daga yan ta'adda amma akayi watsi da maganarsa gashi an gani yanzu.

A cewarsa:

"Rokon da nike maka sabon Aku Uka shine ka hada kawunanmu domin kare kansu daga makiya kasar nan."

"A 2017 da nayi kira ga mutane su kare kansu, wata kwamitin karya da aka kafa tayi bincike kan lamarin tace karya nike saboda babu hujja."

"Yau a kasar nan, ga hujja kowa na gani; yan bindiga daga kasashen ketare na kashe mutane suna kwace musu filaye."

"Ba zan baku makamai ba, ku je ku gano yadda yan bindiga ke samun nasu kuma sai ku samo."

Daga cikin wadanda suka halarci taron mika sandar mulkin akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad III, Gwamna Simon Laloong na Plateau dss.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN