Hukumar NSCDC ta sallami jami'anta 15, ta dakatar da 7, ta rage wa 9 mukami, duba dalili
Hukumar tsaron NSCDC, ta kakabawa jami'an hukumar guda 31 takunkumi kan wasu laifuka.
Kwamandan hukumar NSCDC Dr Ahmed Audi ne ya sanar da matakin ladabtarwar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin hukumar Olusola Odumosu a ranar Litinin a Abuja.
Audi ya ce 15 daga cikin jami’an an sallame su, bakwai kuma an dakatar da su, tara kuma aka sanya su yin ritaya na tilas yayin da daya kuma aka yanke masa hukuncin kisa.
Ya ce matakin ladabtarwar ya samu amincewar hukumar tsaro ta Civil Defence, gyaran fuska, kashe gobara da hukumar shige da fice.
Audi ya bayyana cewa an hukunta jami’an ne bisa laifukan da suka hada da satar ayyuka, hada baki, karbar kudi, jabu, rashin gaskiya da zagon kasa ga tattalin arziki da dai sauransu.
Wadanda aka kora sun hada da Mataimakin Sufeto na Corps I daya, Mataimakin Babban Jami’in Hukumar guda biyu, Mataimakin Sufeto na Corps (AIC), Mataimakin Sufeto na Corps uku (CAIII), CAII biyu, CAII daya, Insifeto Corps daya da AIC daya.
“Jami’an da aka dakatar sun hada da mataimakan kwamandoji biyu, mataimakin kwamandan rundunar guda uku, mataimakin Sufeto na Corps II da CAII daya.
Ya kara da cewa "Hukumar ta kuma amince da dakatar da wani Sufeto na Corps (IC) da kuma rage IC guda daya," in ji shi.
Hukumar ta CG ta ci gaba da cewa matakin ladabtarwar wani bangare ne na matakan kawar da miyagun iri domin tabbatar da ladabtarwa.