Hukumar DSS ta kama Sojan Nijeriya da ake zargi da bayar da hayar bindigarsa AK47 ga 'Ya ta'adda a Abuja.
Daga Ismail Mohammad Goje.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta DSS sun kama Jami'in Tsaron Soja da aka ajiye yake aiki a Muhammadu Buhari Cantonment dake tungan maje cikin birnin tarayyar Abuja da zargin bada haya da kuma saida Bindigu wa masu Garkuwa da Mutane.
An kama shine a makon daya gabata a wuraren dangoki park dake zuba tareda hadin gwuiwar Yan Bangan Sakai dake wannan wurin.
A bayanan rahoto Jami'in Tsaron Sojan ya bada hayar Bindiga wa masu Garkuwa da Mutane akan KuÉ—i N300,000 awani Aikin da masu Garkuwa da Mutanen su kayi, awani Aikin kuma N200,000 a Kudin Hayar Bindiga guda daya.
A rashin sa'ar Jami'in Tsaron Sojan, Masu Garkuwa da Mutanen sun ambaci Sunan sa a matsayin mai basu Makami na Bindiga. Sun kira sa akan wata harkar Bindigun AK47 akan zasu siya N3,000,000 inda nan take ya yarda ya fada.
Sunje inda sukayi yarjejeniyar haduwa a Zuba suka dauki matsaya, shi kuma ya taho a Motar sa domin basu Makaman ananne Jami'an Tsaron su kayi Wuf dashi. An samu Bindiga Kirar AK47 da kuma Bindiga Kirar Magazine Mai Cike da Harsasai Talatin a Motar sa.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI