Type Here to Get Search Results !

Gwamna Wike ya kara adadin mataimakansa na musamman daga 28000 zuwa 50000

Gwamna Wike ya kara adadin mataimakansa na musamman daga 28000 zuwa 50000


Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kara yawan mataimakansa na musamman kan harkokin siyasa daga 28,000 zuwa 50,000.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Kelvin Ebiri, ya fitar a ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba.

“Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike ya sake duba nadin mataimaka na musamman kan sassan siyasa daga 28,000 (Dubu Ashirin da Takwas) zuwa 50,000 (Dubu Hamsin),” in ji sanarwar.

Idan dai za a iya tunawa a ranar Larabar da ta gabata ne Gwamna Wike ya nada mutane 28,000 ga sassan siyasa daban-daban a jihar. Wadanda aka nada sun hada da masu ba da shawara na musamman 14,000, da jami’an hulda da unguwanni 319 da jami’an hulda da kananan hukumomi 40.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies