DA DUMI-DUMI: Daruruwan mazauna karkara sun tsere yayin da ‘yan bindiga suka kai hari kauyuka da garuruwa 40 a Kebbi - ISYAKU.COM

Daruruwan mazauna karkara sun tsere yayin da ‘yan bindiga suka kai hari kauyuka da garuruwa 40 a Kebbi


An kashe mutane da dama yayin da wasu da dama suka tsere zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira bayan da ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyuka da garuruwa 40 a jihar Kebbi.

Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Mu’azu Dakingari, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, 27 ga Oktoba, 2022.

Dangari ya ce Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya kai ziyarar gani da ido sansanin ‘yan gudun hijira da ke makarantar Government Day Secondary School Mahuta da Model Primary School, Isgogo a Masarautar Zuru a ranar Alhamis, domin jajanta wa wadanda abin ya shafa.

“Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, a wannan Alhamis, ya ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Mahuta hedkwatar karamar hukumar Fakai da kuma Isgogo a Masarautar Zuru domin jajanta wa iyalan mutanen da ‘yan bindiga suka kashe a kauyuka fiye da arba’in.  Sanarwar ta kara da cewa a kan iyakar jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara.

“Gwamnan tare da Janar Muhammadu Magoro da Sanata Bala Ibn Na’Allah, sun nuna matukar juyayi da damuwarsu kan lamarin, inda ya shawarci iyalan wadanda abin ya shafa da su kara imani da Allah a matsayin majibincin rahama da jin kai.

Ya yi alkawarin cewa gwamnatin sa za ta kai ga wadanda abin ya shafa yadda ya kamata, musamman don sake tsugunar da su a garuruwa da kauyukan su cikin gaggawa.

“Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya umurci hukumomin da abin ya shafa da su samar da kayan abinci, magunguna da sauran muhimman abubuwa ga ‘yan gudun hijira,” inji shi.

Dakingari ya ce Gwamnan ya bayar da umarnin soke biyan kudin makaranta da kuma harajin PTA domin a ba yaran ‘yan gudun hijira damar zuwa makaranta.

CPS ya ce kauyuka da garuruwan da abin ya shafa sun hada da Ba’are, Iri, Barbaro, Mai Kende, Tungar Gambo, Usheri, Garin Hausawa, Ahuri, Doro, Babban Rafi, Jonga, Hulu, Sago, Adaga da Agwala.

Sauran a cewarsa, sune Masama, Gulori, Arewa, Gurguza, Sabla, Mai Danga, Ucheri, Sangi, Tungar Dutse, Maidaji, Maidaji Gari, Chasgu, Golo Ingarde, Lonka, Ambu, Adaka, Saminaka da Sabon Birni duka dake cikin kananan hukumomin Fakai da Zuru.

Sauran kauyukan da suka rasa matsugunansu a Zuru sun hada da Badi, Kwalo, Rafin Gora I, Muhaye, Isgen, Ganuwa, Rafin Gora II, Ulasa, Dago, Bachuchu, Rafin Gora III, Uli Zamfara.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN