Da dumi-dumi: Yan sandan jihar Kebbi sun kama mutumin da ake zargi ya yi wa 'yar uwarsa mai tabin hankali fyade, wani kuma ya yi wa yar shekara 8 mai tallar kosai fyade

Yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi ya yi wa 'yar uwarsa mai tabin hankali fyade a jihar Kebbi


Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata fyade a wasu abubuwa guda biyu da suka faru a jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta rewaito cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Alhaji Ahmad Magaji-Kontagora ya shaida wa manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Larabar da ta gabata cewa daya daga cikin wadanda ake zargin ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara 8 fyade yayin da dayan kuma ya yi wa ‘yar uwar sa mai matsalar tabin hankali fyade.

“Wani Danjuma Tanko mai shekaru 30 da ke kauyen Zariya Kala Kala-Kala, karamar hukumar Koko/Besse, ya dauki wata yarinya ‘yar shekara takwas mai adireshi daya da take siyar da kosai a gidan wani Umaru Dauda, ​​sannan ya yi lalata da ita da karfi, ya kuma ba ta N200.

“Daga baya, wanda ake zargin ya kuma bai wa Dauda N200 saboda amfani da dakinsa wajen aikata mugun nufinsa.

"Har yanzu ana binciken shari'ar kuma za a gurfanar da shi gaban kotu da zarar an kammala bincike," in ji shi.

Kwamishinan ya ce lamarin ya faru ne a ranar 16 ga watan Satumba da misalin karfe 1:00 na rana.

Ya ce fyade na biyu ana zargin wani Bashir Ibrahim na garin Kangiwa ne ya aikata a ranar 26 ga watan Satumba.

A cewarsa, wanda ake zargi ya dauki ‘yar’uwarsa marar hankali ya Kai ta a cikin magudanar ruwa kuma ya yi lalata da ita da karfi.

Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa Kotu bayan bincike.

Magaji-Kontagora ya yi kira ga jama’a da su rika sanya ido a kan wuraren da suke kewaye da su domin dakile faruwar hakan tare da taimaka wa rundunar da bayanai masu amfani a kan wadanda ake tuhuma. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN