Da alamu Gwamna Bagudu zai biya kudin hutu ga ma'aikatan jijar Kebbi kafin 31 ga watan Oktiba, zai kara shekarun ritayar Malamai zuwa 65

Da alamu Gwamna Bagudu zai biya kudin hutu ga ma'aikatan jijar Kebbi kafin 30 ga watan Oktiba, zai kara shekarun ritayar Malamai zuwa 65


Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu, ya ce Gwamnatinsa ta kafa wani kwamiti da zai tsara yadda za a bi wajen kayyade shekarun ritayar malamai zuwa shekaru 65.

NAN ta ruwaito Bagudu ya bayyana hakan ne a Birnin Kebbi ranar Litinin lokacin da ya bayyana bude taron kwamitin zartarwa na kungiyar kwadago ta Najeriya NLC.

Ya ce Gwamnatin jihar za ta duba yiwuwar biyan kudaden tallafin hutu ga ma’aikata a ranar 31 ga watan Oktoba ko kuma kafin ranar.

Bagudu ya amince da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Gwamnatinsa da kungiyoyin kwadago a jihar.

A cewar Gwamnan, Gwamnatin jihar kuma tana samun goyon bayan dukkanin ma’aikatan gwamnati a jihar.

Ya kuma yaba da irin goyon baya da hadin kai da kungiyoyin kwadago ke bayarwa a jihar tun bayan hawansa mulki.

Bagudu ya tuno da cewa Gwamnatin jihar ta kaddamar da dokar siyan kayayyakin Gwamnati tare da soke hukumar bayar da kwangila ta jihar.

"Wannan matakin ya rage girman ikon Gwamna da mataimakinsa kuma ya mayar da shi ga kwamishinoni da shugabannin ma'aikatu, sassan da hukumomi," in ji shi.

Bagudu ya yaba da irin namijin kokarin da shugaban NLC, Mista Ayuba Wabba ya yi, inda ya bayyana shi a matsayin mai himma da kishin kasa.

Ya yabawa kungiyar NLC bisa yadda ta karrama jihar ta hanyar gudanar da taron a Kebbi.

Bagudu ya kuma yabawa shugabannin kwadago bisa hadin kai da daya daga cikin nasu dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC, Dr Nasiru Idris.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN