A cewar Migrant Rescue Watch, ‘yan sanda sun kai samame a wani gida a gundumar Kufra inda suka kama matan da laifin karuwanci.
An kuma kama wani dan Najeriya da aka ce dan fashi ne yayin samamen.
‘’Yan sanda biyo bayan bincike da sammacin mai gabatar da kara sun kai samame wani gida a Kufra tare da kama wasu bakin haure 9 da suka hada da mata 8 ‘yan asalin Najeriya bisa zargin karuwanci.
Dukkansu an mika su ga hukumar tsaro domin hukunta su. kungiyar ta sanar da haka a ranar Alhamis, 6 ga Oktoba, 2022.
Rubuta ra ayin ka