Yanzu yanzu: Matar da ake zargi da kashe tsohon mijinta a Birnin Kebbi jihar Kebbi ta fadi yadda lamarin ya faru (Bidiyo/Hotuna)


Matar da ake zargi da kashe mijinta a rukunjn gidajen Aliero quarters a Gwadangaji na jihar Kebbi ta yi bayanin yadda lamarin ya faru. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya ruwaito.

Farida Abubakar ta yi bayani ga manema labarai yayin da rundunat yan sandan jihar Kebbi ta gabatar da wadanda ake zargi da aikata laifuka a jihar a hedikwatar Yan sanda da ke Gwadangaji ranar Talata 21 ga watan Satumba 2022.

Ta ce " Na je gidan tsohon mijjna ne domin in mayar mashi da yarinyar da muka kuma in karbi kudin magani don za a kai ta asibiti".

"Tare da shi muka shiga gidan. Shi da kanshi ya kulle gidan". 

" An same ni a baya na boye a cikin keji da ake kiwo domin na tsorata da abin da na gani. Na gan shi a kwance cikin jini, kuma daga ni sai shi muka shiga gidan sai na rude kuma ban gan wadanda suka yi mashi abun ba. Sai na ji tsoro na koma can na boye".

" Bamu yi fada ba, ko magana bamu kare ba abun ya faru.

Kakakin Yan sandan jihar Kebbi SP Nafi'u Abubakar ya ce rundunar Yan sandan jihar Kebbi tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin tare da nufin komo duk wadanda ake zargin suna da hannu a lamarin Kuma za a gurfanar da Farida a gaban Kotu.

Latsa nan ka kalli bidiyo

Latsa nan ka kalli Hotuna

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN