Yan bindiga sun kutsa Masallacin Juma'a ana tsakar Sallah a Zamfara sun yi awon gaba da masu ibada da dama


Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama a lokacin Sallar Juma’a a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba, bayan sun mamaye wani Masallaci a unguwar Zugu da ke karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara. 

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun boye bindigunsu a cikin tufafin su, inda suka kutsa cikin Masallacin a lokacin da Limamin zai fara gabatar da huduba.

An ce masu kutsen sun ce wadanda ke wajen Masallacin su shiga ciki.

“Lokacin da suka yi wa Masallacin kawanya sai suka bukaci wadanda suke wajen da su shiga cikin Masallacin, suka shaida wa masu ibada cewa sun zo ne domin a sako wasu da aka kama,” wani mazaunin garin mai suna Abubakar ya shaida wa Daily trust.

“Ba wanda ya gansu dauke da bindigogi kuma mutane da yawa sun dauke su a matsayin masu ibada, babu wanda ya kula su saboda sun boye bindigogi.

“Sai dai jim kadan da shigewa cikin Masallacin, sai suka fito da bindigu tare da yin harbin gargadi, inda suka garzaya da jama’ar cikin daji amma wasu daga cikin Masallatan sun yi nasarar fita daga Masallacin domin tsira da rayukansu.

“Malamin na cikin wadanda aka yi garkuwa da shi amma Imam ya samu kubuta daga harin.

"An kuma yi awon gaba da wasu da suke wajen Masallacin, saboda ba a san su ba cewa wasu dauke da Makamai sun dauki matsayi a waje, inda suka yi harbin iska da dama sannan suka koma daji tare da wadanda aka kama." Majiyar ta kara da cewa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN