Tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ya magantu kan makomar Najeriya, ya ce...


Tsohon shugaba kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) ya shawarci al'ummar kasar su zama masu kwarin gwiwa da kyakkyawan fata duk da matsalolin da Najeriya take ciki. Shafin BBC Hausa ya ruwaito.

Najeriya in ji shi, za ta ci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa guda.

Janar Babangida na wannan jawabi lokacin zantawa da manema labarai a Minna kafin bikin cikar Najeriya shekara 62 da samun 'yanci, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels ya ruwaito.

Don ganin haka, Janar Babangida ya ce akwai bukatar kowa ya kara himma.

Ya yaba wa kokarin gwamnatoci daban-daban a Najeriya wajen ganin kasar ta ci gaba da zama dunkulalliya, ya kuma yi kira don samun karin nasarori.

Ya ce burinsa shi ne ya ga Najeriya ta zama kasa mai karfi da yalwar arziki da hadin kai ta yadda zaman lafiya zai zarce komai.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN