Type Here to Get Search Results !

Sama da mutane 20 ne ake fargabar sun mutu a fashewar tankar mai a Kogi


Sama da mutane ashirin ne suka kone kurmus a lokacin da wata tankar mai dauke da man fetur ta fashe a Ankpa hedikwatar karamar hukumar Ankpa a jihar Kogi.

Rahotanni sun bayyana cewa, motar dakon mai ta rasa yadda za ta yi, sakamakon gazawar birki, inda ta fada kan gadar kogin Maboro kafin ta fashe.

Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Laraba, 28 ga watan Satumba.

Idon ya ce: "Wannan shi ne babban bala'i na biyu a Ankpa cikin wannan watan. Wannan shi ne mafi muni. Sama da mutane 20 ne suka kone kurmus, wasu ba a iya gane su ba.

“Da yawa daga cikin wadanda aka murkushe su, sassan jikinsu sun warwatse a ko’ina, an debo sassan gunduwa-gunduwa, aka sanya su a cikin jakunkuna.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kogi, Stephen Dawulung, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce har yanzu ba a iya tantance adadin wadanda suka mutu.

“Yara na suna can suna hada bayanai, har yanzu ba mu san adadin wadanda suka mutu ba, wata motar dakon tanka, bas daya da motoci uku, babura guda uku lamarain ya rutsa da su.” Inji shi.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Hollywood Movies