Rabaran Fada ya tona wani asiri game da auren mata biyu daga bisani ya yi murabus, duba abin da ya ce


Wani babban Bishop na cocin Anglican dake Nnewi jihar Anambra, Rabaran Fada Ogbuchukwu Lotanna, ya yi murabus daga kujerarsa a Cocin.

Rabaran Fada Lotanna, a jawabin murabus dinsa yace ya samu sabon umurni na ya kwadaitar da mutane kan auren mace fiye da daya don a rage zinace-zinace cikin al'umma, rahoton Punch.

A cewarsa, auren mace fiye da guda ba haramun bane sabanin abinda ake tunani.

Yace Ubangiji na son mutane su auri mata fiye da daya maimakon neman matan aure da yan mata.

Yace Coci ta dade tana boye hakan ga mambobinta kuma lokaci ya yi da za'a fadawa mutane gaskiya.

Ya yi kira ga Maza su auri 'yan matan da suke lalata dasu don kada su shiga wuta rana gobe Kiyama, riwayar TheNation.

Ya ce zai kafa sabuwar cocinsa mai suna "Gideonites”.

A cewarsa:

"Ko shakka babu cocina musamman na Anglican sun dade suna haramtawa mutane auren mace fiya da guda, amma Ubangiji ya bude idona kuma na fahimci gaskiya hakan ba laifi bane."

Har yanzu cocin Anglican na Nnewi bata yi tsokaci kan murabus din Fada Lotanna ba.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN