Mutum daya ya mutu sakamakon ruftawar gini a Jigawa, duba yadda ta faru


Wani gini da ya ruguje da sanyin safiyar ranar Asabar 17 ga watan Satumba, a karamar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa, ya yi sanadin mutuwar akalla mutum daya. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:47 na safiyar ranar Asabar.

Ya bayyana cewa yayin da mutum daya ya mutu nan take, wasu da dama kuma sun jikkata. An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Birniwa domin duba lafiyarsu. 

Adam ya kara da cewa ‘yan sandan ba su yi zargin wani shiri ba saboda ginin da ya ruguje an gina shi da laka.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN