Ko ka san wani abu akan cutar da ake kira hernia (kaba)

Ko ka san wani abu akan cutar da ake kira hernia (kaba)


Cutar Hernia wacce ake cewa kaba wani yanayi ne da yake samun mutum inda hanjin cikin mutum yake bullawa ta hanyar tissue da tsokar jiki (bangon ciki),wanda wannan tissue din sune suke tare hanji ya tsaya a inda yake.

Kuma shi wannan hernia yana fitowa ne yafi yawa a bangaren ciki da wajen mara ko saman da cibiya (Abdomen) sannan idan ya samu mutum baya tafiya da kansa sai anyi magani.

Kalolin wannan ciwo;

Hiatal hernia

Femoral hernia

Incisional hernia

Inguinal hernia 

Abubuwan da suke jawo wannan cuta;

1. Shekaru

2. Tari wanda yayi Chronic

3. Ciwo wanda ya samu mutum sanadiyyar wani aiki da akai masa, ko mutum yaji ciwo.

4. Mace mai ciki

5. Yawan daukar abu mai Nauyi

Wadan da suke cikin hadarin kamuwa da wannan ciwo;

1. Mace mai ciki

2. Yawan shan taba

3. Tsufa

4. Masu matsalar bayan gida mai tauri,wanda yayi musu chronic

Alamomin gane wannan ciwo.

1. Ganin wani kulluto a ciki ko wani waje daga nan,amma idan ka tanna sai ya rika komawa.

2. Ganin wani kumburi a wajajen ciki ko kasan wajen mara.

3. Jin wani ciwo a wajen matsematsi ,wanda ciwon daga ciki ne.

4. Jin wani nauyi a matsematsi

5. Jin zafi ko wani ciwo a lokacin da mutum yake tari.

Don haka da zarar ka fara jin wasu alamomi daga ciki kayi kokari kaga Likita.

Allah yasa mu dace.

Sirrin Rike Miji

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN