Kada ku zabi masu kashe mutane a 2023 – Jonathan ga ‘yan Najeriya

Kada ku zabi masu kashe mutane a 2023 – Jonathan ga ‘yan Najeriya


Gabanin zaben 2023, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nemi ‘yan Najeriya da kada su zabi masu kashe mutane.

Ya ba da wannan shawarar ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Satumba, yayin wani taro na musamman a Uyo domin murnar cika shekaru 35 da kafuwar jihar Akwa Ibom.

Jonathan ya ce; 

“A shekarar 2023, kada ku yi kuskure wajen zaben masu kisa. Wadanda za su dauki wukake, da bindigogi, da kowane irin kayan aiki su je su kashe mutane saboda siyasa, makiyan al’umma ne. Idan ka yi kisa ka zama shugaba, za ka ci gaba da kashewa ka ci gaba da zama shugaba.

“Mutane za su ci gaba da shan wahala. Ku tabbatar tun daga Majalisar Tarayya zuwa Majalisar Wakilai zuwa Majalisar Dattawa zuwa Gwamna kun zabi mutanen da suka dace a Jihar Akwa Ibom.”

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE