Dan sanda ya bindige tsohuwar matarsa har lahira sannan ya kashe kanshi, bayan ya samu labarin cewa tana shirin auren wani mutum

Dan sanda ya bindige tsohuwar matarsa har lahira sannan ya kashe kanshi, bayan ya samu labarin cewa tana shirin auren wani mutum bayan an raba aurensu da ita


Wani dan sandan kasar Zambiya mai shekaru 29 da haihuwa mai suna Albert Kamasumba ya kashe matarsa ​​mai suna Deborah Kasakula kafin ya harbe kansa har lahira. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Talata, 20 ga watan Satumba, 2022, a garin Pamodzi, da ke Ndola.

Kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito, dan sandan ya harbe matarsa ​​har lahira lokacin da ya samu labarin cewa tana shirin auren wani.

Wani rahoton ya ce Deborah ta bar shi saboda ta gaji da cin zarafi akai-akai. 

Ma'auratan da ke zaune tare a sansanin 'yan sanda na Chifubu an raba aurensu watanni da suka gabata, kuma Deborah ta koma wurin iyaye a cikin garin Kawama na Ndola.

Bayan ya sami labarin cewa tana son auren wani mutum a garin Kitwe, sai ya kai farmaki ya harbe ta kuma wani dan gidan ya ce ‘yar uwarshi ce. 

"An yi zargin cewa bayan ya tashi daga aiki a yau, dan sandan ya je gidan matarsa ​​da ke Kawama ya harbe ta ita da 'yar uwarta daga bisani ya garzaya zuwa ofishin 'yan sanda na yankin Pamodzi inda ya harbe kansa a waje," wani jami'in ya shaida wa manema labarai. 

An sauya shekar dan sandan ne daga ofishin ‘yan sanda na Kawama inda ya kasance a baya, ya zo ne daga wani aiki, sannan ya wuce garin Kawama kai tsaye inda ya harbe matar.

Bayan ya kashe ta, sai ya nufi ofishin ‘yan sanda na yankin Pamodzi inda ya yi wata ‘yar gajeruwar tattaunawa da jami’an da ba a san ko su wanene ba.

Daga nan sai ya ba wa wani jami’in wayarsa ya ce ya ba wanda zai zo ya tambaye shi.

Daga nan sai dan sandan ya fita waje ba tare da jami’an ’yan uwansa sun yi zargin wani abu ba kuma abin da suka ji shi ne harbin bindiga.

Lokacin da jami’an suka garzaya waje sai suka same shi kwance a cikin jini kusa da wani famfon ruwa.

Jami’in hulda da jama’a na asibitin koyarwa na Ndola, Sheona Kamwendo ya tabbatar da cewa asibitin ya karbi gawarwaki biyu na namiji da mace daya mai suna Albert Kamasumba da Deborah Kasakula. 

Ma'auratan sun bar yaro mai shekara daya da wata daya. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN