An gano tare da ceto jariri dan mako biyu da aka sace a asibitin ATBUTH, an maida shi ga mahaifiyarta a Bauchi

An gano tare da ceto jariri dan mako biyu da aka sace a asibitin ATBUTH, an maida shi ga mahaifiyarta a Bauchi


Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) Bauchi, ta ce an kwato jarirai tagwaye dan kwanaki 14 da aka sace a asibitin a Bauchi
.

Dokta Haruna Liman, Shugaban Kwamitin Ba da Shawarar Likitoci (CMAC) na asibitin ya bayyana haka, a lokacin da yake mika jaririn ga mahaifiyar ranar Talata a Bauchi.

Ya ce an sace jaririn daga hannun mahaifiyar a asibiti bayan kwana takwas da haihuwa. 

“An sace jaririn ne a ranar 21 ga Satumba, 2022 da karfe 4:30 na yamma daga hannun mahaifiyar da ke karbar magani a asibiti.

“An ceto yaron a yau, 27 ga watan Satumba da misalin karfe 1:00 na rana cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.

“Muna godiya ga Allah da kokarin da jami’an tsaron cikin gida na asibitin, DSS, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka yi wajen ceto jaririn,” inji shi.

Dakta Liman ya ce tuni jami’an tsaro suka cafke wata mata da ake zargi da kitsa wannan mugunyar aikin.

“A halin yanzu ana yi mata tambayoyi, abin da muka sani kenan bayan jami’an tsaro sun mika jaririn ga Hukumar Kula da Asibiti.

“Yanzu muna mika tagwayen jaririn mako biyu ga mahaifiyar da iyalan cikin koshin lafiya.

Shugaban ya bayyana cewa hukumar za ta yi nazari kan tsarin tsaro na asibitin tare da sanya karin na’urorin fasahar tsaro a asibitin.

Hakimin Bauchi, Alhaji Nura Jumba, ya bukaci mahukuntan asibitin da su sake duba tsarin tsaro na asibitin domin gujewa sake aukuwar irin haka.

Ya yi alkawarin cewa a ko da yaushe shugabannin gargajiya za su wayar da kan al’umma kan lokutan da suka dace na ziyartar marasa lafiya a asibiti.

Jumba ya bukaci mahukuntan da su kulla alaka da iyali, da nufin ganin sun fahimci halin da suke ciki.

Da yake mayar da martani a madadin iyalan jaririn, Malam Shitu Kalid ya bayyana jin dadinsa ga mahukuntan asibitin bisa damuwarsu da kuma jami’an tsaro na ganin an dawo da jaririn.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN