Ambaliyar ruwa ta yi sanadin tonewa tare da kwashe gawarwaki 500 daga Makabarta a jihar Neja – Babban Limamin

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin tonewa tare da kwashe gawarwaki 500 a jihar Neja – Babban Limamin


Al’ummar garin Mariga da ke karamar hukumar Bariga a jihar Neja na neman gawarwaki sama da 500 da ake zargin ambaliyar ruwa ta tafi da su. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Babban Limamin Masallacin Mariga, Alhaji Alhassan Na’ibi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta wayar tarho ranar Talata.

Ya ce "Yanzu muna neman gawarwaki sama da 500 da aka binne a wata makabarta a garin Mariga wadanda muka yi imanin cewa ambaliyar ruwa ta Mariga ta tafi da su."

Nai’bi ya ce al’ummar yankin sun shiga rudani, domin sai da aka kwashe wasu gawarwaki kimanin 100 daga makabarta zuwa wata makabartar domin dakile faruwar lamarin.

Babban Limamin wanda ya alakanta matsalar da ayyukan masu hakar ma’adanai da ke kusa da makabartar, ya koka da cewa ba su taba fuskantar irin wannan yanayin ba a cikin shekaru 60 da suka wuce na makabartar.

Sai dai ya yi kira ga gwamnatin jihar Neja da ta gaggauta kawo musu dauki domin dakile lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN