Yanzu yanzu: Kotu a Birnin Kebbi ta yanke wa matashi hukuncin daurin shekara 2 da bulala 40 sakamakon neman matar aure da niyyar yin lalata


Babban Kotun Majistare ta 1 da ke zamanta a garin Birnin kebbi ranar Talata, ta daure wani matashi mai suna Mubarak Lawali a Kurkuku, sakamakon neman matar aure da niyyar yin lalata da ita. Shafin labarai na isyaku.com ya tattaro.

Kotun ta daure Mubarak shekara biyu a Kurkuku tare da biyan tarar naira dubu hamsin N50.000, da kuma biyan diyyar hidimar wanda ya shigar da kara naira dubu hamsin N50.000, da kuma bulala arba'in.

Tun farko dai, dan sanda mai shigar da kara Safeto Jibril Abba, ya gaya wa Kotu cewa:

" A cikin watan Yuli a garin Kamba da ke karamar hukumar Dandi a jihar Kebbi, Mubarak ya tunkari wata matar aure mai suna Farida Aliyu, matar Alh. Aliyu Abubakar, ya bayyana mata manufarsa ta neman yin lalata da ita, duk da cewa matar aure ce. Kuma ya tura mata hotunan batsa ta WhatsApp a wayar salula".

Safeto Jibril ya ce wannan ya saba wa sashe na 370 na dokar Penal code na jihar Kebbi 2021.

Alkalin Kotun, Cif Majistare Hassan Muhammed Kwaido, ya tambayi Mubarak ko haka zancen yake, kuma ya amsa laifinsa a gaban Kotu nan take. 

Bisa wannan dali, Lauyan Mubarak ya nemi Kotu ta yi wa Mubarak sassauci duba da cewa bai taba aikata wani laifi ba kuma wannan ne karo na farko a rayuwarsa. Ya kuma gaya wa Kotu cewa wanda ya tsaya wa mutumin kirki ne a cikin al'umma.

Sakamakon haka Kotu ta daure Mubarak Lawali shekara biyu a Kurkuku, tarar N50.000, biyan diyyar N50.000 da kuma bulala 40, bisa tanadin hukuncin sashe na 370 na dokar Penal code da kuma tanadin wasu sassan hukunci na dokokin ACJA 2021 na jihar Kebbi.

Sai dai Mubarak ya bukaci a kira masa iyayensa domin ya gana da su. Bayan isar Mahaifinsa wajen da yake a dakin Kotu, sai Mubarak ya fashe da Kuka, hawaye shara-shara yana cewa "Wallahi ban taba aikata wannan laifi ba"  a lokacin da yake jiran a yi masa bulala 40 tare da tasa keyarsa zuwa Kurkuku inda zai shafe shekara 2 jere bayan biyan tara da diyya. 

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN