Tsarin masarautu a Najeriya yana aiki ne a karkashin kananan hukumomi kuma gwamnonin jihohi suna da ikon girka sarakuna da tsige sarakunan gargajiya a jihohinsu.
Tun bayan dawowar jamhuriya ta hudu a Najeriya tsarin ya gamu da tsige sarakunan gargajiya kusan 10 a fadin kasar, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Ga jerin sunayen sarakunan gargajiya da aka cire a Najeriya:
Sanusi Lamido Sanusi II - Emir of Kano, Kano
Oluwadamilare Adesina Osupa - Deji of Akure, Ondo
Abubakar Atiku - Emir of Zurmi, Zamfara
Hussaina Umar - Emir of Dansadau, Zamfara
Sulaiman Ibrahim - District Head of Birnin Tsaba, Zamfara
Mustapha Jokolo - Emir of Gwandu, Kebbi
Cif Monday Frank Noryea - Sarkin gargajiya na masarautar Baabe, jihar Rivers
Sarki Joseph Okor - Ivi na Akaeze, Ebonyi
Eze Michael Orji - Ebonyi
Aslem Aidenojie - Onojie na Masarautar Uromi, jihar Edo (Adams Oshiomhole ya cire shi daga cin zarafin mata amma daga baya Gwamna Godwin Obaseki ya dawo da shi)
A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsige sarakunan gargajiya da gwamnonin jihohi ke yi na kara samun karbuwa a sararin samaniyar Najeriya.
A lokacin da ake maganar gwamnonin da suka tsige sarakuna a jihohinsu, ko da yaushe za a tuna cewa tsige tsohon Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan CBN, Lamido Sanusi.
Sai dai kuma, Sanusi ba shi ne na farko ba, kuma ba shi ne sarkin gargajiya na karshe da wani gwamnan Najeriya ya sauke tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999 ba.